Joystick Hausa Novel Complete

joystick hausa novel complete

Joystick hausa novel complete by Salman Haris is a gripping Hausa love story that delves into themes of love, societal expectations, and determination. Set in a typical Nigerian environment, the novel follows the life of Ahmad, popularly known as "Joystick," and his passionate pursuit of Zainab, a beautiful widow he meets by chance. What unfolds is a whirlwind romance that tests the boundaries of tradition and personal desire.

Joystick hausa novel complete begins with Ahmad, a merchant, leading a relatively uneventful life until the day he catches sight of Zainab. Her beauty instantly captivates him, and from that moment, Ahmad’s life takes a dramatic turn. Despite Zainab’s past and the fact that she is a widow, Ahmad is determined to win her love. His pursuit, though initially lighthearted, soon transforms into a deep emotional journey.

Salman Haris does a remarkable job of portraying Ahmad joystick's emotional turmoil after Zainab’s father rejects his marriage proposal due to societal norms. The author carefully explores the tension between Ahmad’s unwavering love and the societal prejudice that surrounds widowhood and second marriages. This conflict drives the narrative forward, creating a gripping and emotional tale that keeps readers invested in the outcome.

Zainab's character is portrayed with grace and dignity. Despite the societal pressures she faces as a widow, she remains strong and composed. Her initial reluctance to Ahmad’s advances feels genuine, and her eventual acceptance of his love after overcoming societal barriers adds depth to her character. Salman Haris highlights the often-overlooked struggles of widowed women in traditional societies, giving the joystick hausa novel complete a thought-provoking edge.

Ahmad, on the other hand, is a compelling protagonist. His transformation from a carefree young man to someone deeply in love and ready to challenge societal norms is both believable and heartwarming. The nickname "Joystick" symbolizes his earlier, carefree persona, but as the novel progresses, we see a more mature side to him. His persistence in the face of rejection is admirable, and his love for Zainab becomes a driving force that propels the story forward.

Joystick hausa novel complete part 1

Haba! Ahmad yau fa satinka guda a gida baka fita ko kasuwa ba, dan Allah ka zubawa zuciyarka ruwan sanyi. Ka hakura da yarinyar nan tunda iyayenta sun hana.

Ahmad Dauda kenan wanda aka fi sani da joystick a wannan complete Hausa novel yana cikin mugun yanayi sakamakon hana shi auren masoyiyarsa Zainab. Yau kwanansa biyar kenan a gida baya fita ko ina, kullum yana daki yana bakin ciki. Bari na baka masomin wannan lamari na Ahmad joystick.

Wata rana Ahmad ya dawo daga kasuwa kamar yadda ya saba, ya shiga cikin gida yaci abinci sannan ya huta. Misalin ƙarfe huɗu na yamma yasa kayansa ya kama hanyar zuwa wajen abokansa, da yake wajen bashi da nisa bai tafi da babur dinsa ba, yana tafiya yana yan kalle kallen garin. Kamar ance Ahmad dan juyo, ai waiwayen da zai yi ya hango wata kyakkyawar mace, fara tas da ita kana ganinta kaga irin fulanin adamawa. 


Joystick hausa novel complete
Joystick hausa novel complete part 1

Tanada dogon wuya mai annuri da jan hankali, hancinta kuwa tamkar ita tayi abinta, tanada karamin baki, ga dara daran idanu. tanada jiki irin wanda duk wani namiji ya ganta saita burgeshi, daɗin da ɗawa gata doguwa kuma ba yar lukuta ba. Ahmad joystick ya zuba mata ido ko kiftawa baya yi, yadda kasan wani gunki haka ya zama a tsaye. 

Wannan baiwar Allah ta fuskanci duk abinda ke faruwa, kawai sai tayi murmushi tayi gaba abinta, tamkar an watsawa Joystick ruwan sanyi haka ya wani zabura, sai ya ɗan sosa kai, sannan ya cigaba da tafiya. Zuciyarsa ta dinga bugawa da sauri da sauri, yace a ransa gaskiya bazan iya barin wannan dama ta wuce ni ba.

Ita dai wannan mace tuni tayi nisa kuma bakuwa ce wacce suka zo biki, idan ka kalli fuskanta tanada matukar kyau amma kuma ba budurwa bace, Sunanta Zainab sannan yar unguwar Kundila ce, dalilin da yasa Zainab zama zawara kuwa mijinta ne ya rasu ko cikakkiyar shekara ba'a yi dayin aurenta ba. 

joystick hausa novel complete part 2

Da Ahmad yaga wannan mace tayi masa nisa, sai ya soma sauri domin ya tardo ta, har wani gudu gudu yake duk da yasha wanka da wata bugaggiyar shaddarsa, kuma yayi kyau sosai. Da karasowa kusa da ita sai ya mata sallama ' ta amsa sannan ta fuskance shi, sai yayi mata murmushi itama martanin murmushin ta mayar masa, 

Da Allah wannan kyakkyawar yarinya ina da tambaya ne a gareki, tace to Allah yasa na sani, ya ƙara yi mata murmushi. Sannan yace tunda nake a rayuwata ban taɓa ganin mace mai cikar kamala irinki ba, tace ko? yace wallahi babu ko kokwanto a cikin abinda na faɗa, ke kyakkyawa ce kuma mai siffar mutanen kirki. Cewa tayi Nagode amma ina sauri meke tafe da kai Ahmad joystick yace 'Dan Allah kawai ya sunanki?' 

Murmushi tayi sannan tace yanzu duk wannan maganganu naka kawai sunana kake so ka sani? Ahmad cewa yayi aini jin sunan kaɗai wata babbar nasara ce, ta ƙara yin murmushi sannan tace sunana Zainab. Joystick yace Allah mai babban suna. 


Joystick hausa novel complete
Joystick hausa novel complete part 2 

Shin zan iya ƙara neman wata afuwa? tace OK menene? anan unguwar kike? tace a'a munzo gidan yan uwanmu biki ne. Gaskiya dai dama ban taɓa ganin kyakkyawa irinki a unguwar nan ba, to ki taimakin da lambarki mana ko gaisawa mu dinga yi. Zainab cewa tayi gaskiya bana ba wanda ban sani ba lamabata. 

Ahmad joystick ya kalleta cikin ido yace "koda mutumin yana sonki" wata dariya Zainab ta saki sannan tace EH. Sai ta ɗan yi gaba ta cigaba da tafiya tana murmushi, Ahmad ya fuskanci kawai wasa take masa sai ya bita yasha gabanta yana dariya yace ai kuwa sai kin bani lamba, yaya sunanka? Zainab ta tambaya: Sunana Ahmad joystick. 

Tace umm nice name, Amma wallahi sauri nake bani wayarka, ya mika mata waya ta saka masa lamba, nan suka yi sallama ya koma inda ya fito. Saboda tsabar farin ciki Ahmad ya manta ashe wajen abokansa zai je domin har ya canja hanya. Can ya gane ashe ba hanyar yake bi ba. Sai yayi wa kansa dariya sannan ya kama hanyar dai dai. Da zuwansa majalisa suka tafa da abokansa sannan suka hau labaran duniya yadda abokai keyi. 

joystick hausa novel complete part 3

Abokansa suna ta surutu yayinda hankalin Ahmad joystick ya faɗa kogin tunanin kyakkyawar gimbiya Zainab. Bayan sallar Isha ya dawo gida, bayan ya gama abinda zai yi ya shiga dakinsa domin ya kwanta. Ya janyo wayarsa da nufin ya kira Zainab, yaji wayarta switch off ya ƙara kira yaji switch off. 

Nan da nan hankalinsa ya tashi, zuciyarsa ta soma bugawa da karfi, karfa Zainab lambar karya ta bani cewar Ahmad a ransa! oh my gosh! nan yaji wani ciwon kai ya rufe shi, hada zazzaɓi a haka yasha magani sannan yayi bacci. Washe gari tun da safe ya kira wayar Zainab amma yaji yanzu ma wayar bata shiga kwata kwata, haka ya hakura ya dauki babur dinsa ya tafi shagonsa dake kasuwa.

A wannan rana haka Ahmad joystick ya wuni a kasuwa cikin zullimi domin duk ya canja, kamar ya saba dawowa haka ya dawo gida. A lokacin ma ya ƙara gwadawa amma yaji shiru. Shikenan ya hakura ya cigaba da harkokin gabansa. Bayan kamar kwana biyu Ahmad ya dawo dai dai amma har yanzu yana matukar kaunar Zainab. 


Joystick hausa novel complete
Joystick hausa novel complete last 

Yana kwance a dakinsa da rana ƙanwarsa Maryam ta kawo masa abincinsa na rana, ya dauko wayarsa yace "in dai na gwada lambar nan yanzu bata shiga ba to ba zan kara kira ba, kuma zan gogeta" ai da soma kiran wayar sai yaji ta shiga, zuciya ta buga dum dum kawai sai yaji ance " Salama alaikum" cikin wata shakakkiyar murya Ahmad joystick ya amsa, "wa'alai....ku". 

Yace ina magana ne da Zainab, cewa tayi Ahmad ne? wallahi nine yace, Zainab tace " se yau zaka kirani ko? Ahmad kamar zai yi kuka yace " Wallahi Zainab ina matukar son ki". Zainab ma cewa tayi wallahi Ahmad tun a ranar da muka haɗu naji ina sonka kawai dai na boye ne.

joystick hausa novel complete last part 

Nan suka soma sabuwar soyayya, suna cikin maganganu tace masa "Ahmad Nifa zawara ce" Ahmad yayi shiru...... sannan yace Zainab wallahi ina sonki a haka kuma zan aure ki.

Bayan sallar la'asar Ahmad joystick ya kama hanyar unguwar su Zainab, wato rijiyar lemo, ta amsa kwatance har kofar gidansu. Gida ne mai kyau na masu rufin asiri, da zuwansa suka yiwa juna murmushi ta taho izuwa gareshi cike da farin ciki da fara'a, kamar waɗanda aka yiwa albishir da aljanna haka suka zauna suna kallon juna.

Ahmad cikin fara'a yace ya naga yau kin ƙara kyau ne? cikin dariya Zainab kai ne ai naga ka canja kamar ba kai ba. Suka riƙe hannun juna sannan suka cigaba da hirarsu ta masoya. Shakuwa ta kai shakuwa Zainab da Ahmad joystick sun shaƙu har maganar aure ta gitta tsakaninsu, amma lokacin da babanta yaga Ahmad joystick sai yace ba zai bashi diyarsa ba. 

A wannan hali Ahmad yake zaune a gida yanzu haka, har tsawon yan kwanaki bai fita ko kasuwa ba, bayan babansa ya bashi hakuri, sai yayi ya fita shagonsa, yana cikin cinikayya saiga kiran Zainab, yanzu Ahmad sai ka daina ɗaukar wayata me nayi maka?. Ina so nayi magana da kai, yace ina jinki: kasan cewa baba ya hanaka aure na ne saboda kai saurayi ne ni kuma bazawara, wannan shine dalilin?? 

Nan da nan Ahmad joystick ya rufe shago ya kama hanyar gidan su Zainab, yayi sallama da mahaifinta, Ahmad joystick yace baba a haka nake sonta wallahi a haka zan aureta. Baban Zainab yaga Ahmad da gaske sai yace shikenan na baka Zainab Ahmad.

Ya koma gida ya sanar da mahaifinsa, aka saka ranar bikin Zainab da Ahmad, aka sha biki aka kai amarya gidanta, yanzu haka suna can suna zaman aurensu lafiya wato Ahmad joystick da amaryarsa Zainab.

Previous Post Next Post