Romantic Hausa Novels Complete Download

Romantic Hausa Novels Complete Download –

Note! Ba'a sauke littafi a nan.

Romantic Hausa Novels Complete Download

Sannu da zuwa, mai karatu! Idan kana neman romantic Hausa novels complete to download, to ka zo inda za'a nuna maka. Littattafan Hausa Novels musamman na soyayya sun shahara sosai saboda yadda suke cike da shauki, soyayya, da darussan rayuwa iri daban-daban.

Hausa novels suna da muhimmanci a al’adar Hausawa, domin suna bayar da labarai masu jan hankali, kama daga soyayya, rayuwar iyali zuwa kasada a littattafan yaƙi da rikici. Babu shakka, waɗannan littattafai suna jan hankalin masu karatu a ko’ina a fadin duniya – ba kawai a Najeriya ba, har ma a sauran sassan kasashen duniya.


A wannan zamani, sakamakon cigaban fasahar yanar gizo, yana da sauƙi a samu wadannan littattafai a shafukan yanar gizo da dama da blogs. Wanda za ka iya karanta su kyauta ko kuma ka sauke su a PDF domin karantawa a waya, tablet, ko kwamfutarka.


A cikin wannan blog post namu na yau, mun lissafo best romantic Hausa novels complete domin masoya littattafan soyayya. Za ka iya karanta su ko bin link ɗin da muka bayar domin karantawa ko suke cikakken labarin.


Shin ka san cewa?
Marubutan littattafan Hausa suna taka rawar gani wajen cigaban adabin Hausa. Wasu daga cikinsu sun shahara sosai, yayin da wasu sabbin marubuta ke ƙoƙarin kawo sababbin hikimomi a cikin rubuce-rubucensu. Duk da haka, burinsu ɗaya ne – wato shine cigaban adabin Hausa da kuma jin daɗin masu karanta littafinsu.



1. Kuskuren Rayuwa (Life Mistakes) – Zee Yabour

Littafin Kuskuren Rayuwa yana ɗaya daga cikin shahararrun littattafan Hausa. Sunansa a Turanci yana nufin "Mistakes of Life." Marubuciyar littafin, Zee Yabour, tana daya daga cikin shahararrun marubutan Hausa a kafafen sada zumunta.


Excerpt:

"Fitowarta daga bayan gida kenan, tayi picking wayarsa. Cewa yayi, ‘Masoyiya, ina jiranki a dakin baki,’ kafin ta ce wani abu, ya katse wayar. Tayi murmushi, sannan da saurinta ta soma shafa man cream, ta fesa turarenta mai kamshi, sannan ta sanya hijabi wanda ya tsaya mata iya gwiwa. Ba ƙaramin kyau tayi ba, ta kama hanyar zuwa dakin baki."

Karanta cikakken littafin nan



2. Fetta (The Girl Fetta) – Zee Yabour

Wannan littafi yana bada labarin Fetta, wata marainiyar yarinya da ke fuskantar kalubale a rayuwa. Duk da wahalhalun da ta sha, daga ƙarshe ta cimma nasara kuma ta zama mai arziki.


Excerpt:

"Fetta tana wasa a cikin ruwan sama yayin da babanta ke ta kwala mata kira akan ta fito daga cikin ruwan domin kada mura ta kamata. Fetta ta cigaba da wasanta kamar bata ji me babanta yace mata ba. Bayan ruwan ya tsagaita, ta nufo dakinsu domin ganin mahaifinta."

Karanta cikakken littafin nan



3. A Soyayyar Mu (In Our Love) – Hijjart Abdoul

Littafin A Soyayyar Mu yana bada labarin soyayya mai cike da rashin jindaɗi. Labarin yana da sassa 51 domin sauƙaƙe karatu ga masu karatu.


Excerpt:

"Tauraron wannan labari ya girma yaga gidansu babu mace ko daya a cikinsa. Rayuwarsu gaba ɗaya babu mata. Idan ka ga mace a gidan, to ko wata bakuwar ‘yar uwarsu ce, ko kuma ‘yar uwar mahaifinsa. Wannan dalilin yasa makwabta suke kiran su da ‘Gidan Gwauraye.’ Amma kwatsam, ƙaddara ta canza komai."

Karanta cikakken littafin nan



4. Kalbina (My Heart) – Aysha Sona

Kalbina yana nufin "My Heart" a Turanci. Littafin yana da sassa 112, kuma yana daga cikin mafi shahara akan Wattpad.


Excerpt:

"Sunana Hibba, shekaruna duka ba zasu fice ashirin da biyu (22) ba. Ba ni da kowa sai kanina, kuma duk duniya gatanmu ɗaya shine Allah. Shi kadai ne zai fitar damu daga wannan halin da muke ciki."

Karanta cikakken littafin nan



5. Zan Soka A Haka (Love You Like That) – Queenbk2020

An wallafa wannan littafi a watan Yuni, 2020. Duk da cewa marubuciyar ba ta shahara sosai ba, amma littafin ya sami karɓuwa sosai saboda kyakkyawan labarin daya kunsa.


Excerpt:

"A zaune take kamar yadda ta saba cikin jerin Fulani da ke sayar da fura da nono a kasuwa. Tana sanye da saki fari, irin kayan Fulani, kuma duk wanda ya kalleta sai ya ƙara kallonta saboda kyawunta."

Karanta cikakken littafin nan



6. Badakala (Crashes) – Maryamerh Abdul

Littafin Badakala yana kunshe da labarin mata bakwai da suke fuskantar wahala daban-daban a rayuwa.


Excerpt:

"Katafaren wajen shakatawa na Cubana dake cikin birnin Abuja. A cike yake da manya manyan motoci da ababen hawa iri iri. Wasu motocin a manne suke da kasa, sai ka rasa taya suke iya tafiya ba tare da sun gogi kasa ba..."

Karanta cikakken littafin nan



Wasu Karin Littattafan Soyayya da Za Ku Karanta:

7. Mai Sona (My Love)

8. Makauniyar Hanya (Blind Way)

9. Bakar Aya (Black Pit)

10. Matar Uba (Stepmother)

11. Nabeela (The Girl Nabeela)

12. Masifaffen Namiji (Hot Man)

13. Jarrabar Rayuwa (Life Situations)


Idan kana son free romantic Hausa novels complete, waɗanda muka lissafa a sama zaka ji daɗin karantasu. Wannan jerin littattafai na daya daga cikin mafi shahara a duniyar adabin Hausa.


Littattafan soyayya ba kawai domin soyayya ba ne – a'a, suna cike da darussa akan rayuwa, iyali, da zamantakewa. Masu karatu suna matukar ɗokin samunsu saboda suna ɗauke da labaran da ke kama zuciya da gaske.

Previous Post Next Post