Abban sojoji complete hausa novel
Read new novel Abban sojoji complete by Boss Bature, always we're online for you. Enjoy Abban sojoji complete up to the end on our blog.
Abban Sojoji complete is an engaging Hausa novel written by Boss Bature. The story revolves around family ties, love, and the challenges faced by individuals who come from military backgrounds. The author carefully explores the dynamics of authority, discipline, and loyalty that shape the lives of the characters, especially those influenced by the military lifestyle.
The protagonist's journey is captivating, revealing the struggles, triumphs, and personal growth experienced in the context of deep-rooted cultural values. Abban sojoji is immersive, drawing readers into a world of emotions, from tension to heartwarming moments.
Abban sojoji complete (part 1)
Yinin wannan ranar, Sehrish tana jin jikinta cikin yanayi mara misaltuwa. Gashi yanayin shine irin na ni'ima amma kuma da kasala mai tsanani a tattare da ita, wani lalaci ya mamaye ta. aunty Azmee ta sanar da ita cewa bata da aiki yau, ta zauna ta huta kawai, domin yau ranar hutunta ce. Daga wannan bangare zuwa wancan take yawo a cikin gida, zuciyarta cike da tunani kala-kala gameda su Husanna da Jahad. Ga kuma wani irin bugu da zuciyarta keyi mata, kamar tanajin wani abu gameda babban yayansu tun kafin ta ganshi.
Sehrish ta zuba ido tana kallon meatballs din da suke cike cikin plate din da aka ajiye a saman bedside drawer. Ga fresh milk a cikin glass cup. Tayi shiru tana kallon abincin, jikinta a mace yake. Kamshin abincin ya cika dakin, amma a kullum tana jin kamar bata yiwa yan uwanta adalci ba. Yayinda ita take cin abinci mai dadi, su suna cikin mawuyacin hali.
Sehrish ta zauna a saman gadonta, ta lankwashe kafanta, tana tunani. Aunty Azmee ta sake turo kofar ta shigo, hannunta dauke da fresh fruits a cikin wani dan plate.
"Ya dai? Har yanzu baki fara ci ba? Me kike jira?" Aunty Azmee ta tambaya.
Sehrish ta sauke ajiyar zuciya, sannan tace, "Aunty Azmee, zuciyata bata min dadi musamman idan na tuna da yan uwana. Sai naji bana son cin komai."
Azmee ta nuna damuwa, ta zauna gefen gadon Sehrish cikin natsuwa, sannan tace, "Kinyi imani da Allah?" Sehrish ta daga kai tareda cewa, "Eh."
"Inaso a duk_lokacin_da_zaki yi addu'a, ki kasance_mai_cike_da_imani. Kiyi imanin cewa addu'ar da kika yi, Allah ya karbeta. Kada ki taba shakkar hakan, saboda rashin imani yana hanamu samun wani abu. Amma muddin kinyi addu'a kina da imani cewa Allah ya karba, ba tareda kinyi kokwanton cewa anya Allah ya karba ba? Ko kuma saboda ba kiga sakamako nan take ba, kada ki damu. Kawai kisa a ranki cewa duk lokacin da kika yi addu'a, Allah ya amsa, kuma insha Allahu, zaki ga sakamako mai kyau. Zaki samu natsuwa a cikin zuciyarki."
Sehrish ta jinjina kai sannan tace, "Nagode Aunty Azmee. Insha Allah zanyi kamar yadda kika ce."
Murmushi Azmee tayi sannan tace, "Yawwa Rishi na. Yanzu dai ayi mun murmushin kashe zuciya na gani," ta fadi cikin zolaya, tana kallonta.
Abban sojoji complete
(part 2)
Sehrish ta sunnar da kai tana murmushi, itama Azmee murmushi take yi. Azmee ta dauki yankakkiyar abarbar dake cikin plate, ta kai mata a baki tareda cewa, "Bude baki, kici!"
Sehrish ta bude baki tana dariya kadan, sannan Azmee ta zura mata abarbar. Sehrish ta taune, zakin abarbar ya cika mata baki, har ta kama lasar labba. Azmee tace, "Yawwa! Ko kefa, yanzu naji magana. Bari na baki meatballs din a baki."
Cikin_sauri_Sehrish_tace, "A'a Aunty_Azmee, zanci_yanzu. Kun sha aiki, kun gaji, kuma ban taya ku ba."
Azmee ta ce, "Kada ki damu Sehrish. Ni nace ki zauna tunda gasu Chef Ummu, aiki na tafiya yadda ya dace. Ina fatan dai ba kiyi tunanin babban yaya ba yau?"
Azmee ta karasa maganar tana kallonta cikin zolaya. Sehrish_ta_sunnar_da kai_tana murmushi, jin_an_ambaci_sunan_da ke_mata kaikayi_a_cikin_zuciyarta.
"Bani da amsa kenan?" Azmee ta tambaya cikin dariya. "Ni zan tafi yanzu. Kada ki manta, a daren yau kiyi sallolin nafila, ki yi addu'o'i wa yan uwanki da kuma sauran al'ummar Musulmai." "Insha Allah, Aunty Azmee, nagode sosai."
Azmee ta tashi ta fice daga dakin. Hakika Sehrish ta samu natsuwa a ranta, Azmee ta iya kalami masu dadi masu sanyi da ratsa zuciya. Sehrish ta zauna ta dinga cusa fruits din dake gaban ta cikin bakinta. Cikin dadi take shansu, bayan ta gama dasu, ta dauko na meatballs ta shiga dauka tana jefawa a baki. Yaji sosai, yayi dadi. Lokaci zuwa lokaci tana hada da cool milk dake cikin cup, tana kurba.
AUNTY BABBA..
Zaune take a gefen Amani saboda basu tafi ba, suna jiran zuwan babban yayansu. Duk da ita Amani tana cikin garin, amma Abbas ya bata izinin ta zauna ta kwana tunda auntyn tana nan itama. Insha Allahu zuwa gobe sai ta koma gida.
Dukkansu suna sanye da kayan bacci, riga da wando masu kyau. Kowacce ta zubo gashinta, Allah ya albarkace su da kyan gashi.
"Ina sauraronki, aunty na," Amani tayi magana tana kallon auntynta dake gefenta saman gado.
"Shiri na musamman ya kamata mu yiwa lamarin domin cin nasara akan wadannan zafafan guda biyu. Shawo kansu ba abu mai wahala bane, sai dai dole mu hada da shahararrun bokaye, kamar wannan bokan dake kurmin dajin Enugu," inji Aunty Babba.
Amani ta zaro ido tareda cewa, "Aunty, Enugu fa kika ce? Gaskiya akwai wahala wallahi."
Abban sojoji complete last
Dariya_Aunty_Babba_tayi, tace, "A wurinki_ne ba. Ni akan na cimma burina, ba abunda ba zan iya yi ba. Hmmm, ke dai kawai abar kaza cikin gashinta har yanzu baki san wacece yayarki Laila ba."
Amani ta sunkuyar da kai, tana kallon Aunty Babba da tashin hankali. Lamarin ya fara bata tsoro. "Yanzu Aunty, yaushe zaki tafi Enugu?"
Cike da kwarin gwiwa, Aunty Babba tace, "Ni bana aiki cikin gaggawa. A sannu zamu cimma nasara. Amma kafin nan, muna bukatar kudade da yawa. Don tunkarar wannan boka ba abu bane mai sauki. Dole mu hada karfi da karfe. Ki tatsar mana wurin Abbas, nima zan tatso wurin Ishaq. Daga nan zamu yi maganar tafiya."
Shiru Amani tayi, tana jin kasala. Cike_da karaya_tace, "Aunty, ni_fa ina_tsoro_wlh."
Mtswww! Aunty Babba ta ja tsoki, tace, "Ke dallah, wane tsoro? Aje wannan gefe. Ke baki san abinda nake hango mana ba. Muddin muka ci nasara akan babban yayansu da Marshal Omar, to zamu juya dukkanin family din nan yadda muka so." Ta gama magana tana kallon Amani, wadda tayi tsuru-tsuru.
Amani ta sauke ajiyar zuciya, tana kokarin yin magana, sai wayarta dake saman pillow ta soma ringing. Da sauri ta duba sunan, "Babyna" ya bayyana. "Aunty Babba tace, "Halan Abbas ne?" Amani tace, "Eh shine."
"Yawwa, maza ki daga. Ki kashe masa murya kina masa ladabi, ko munci nasara akan kudin da muke bukata."
Amani ta amsa da "to," tareda amsa call din, ta kara a kunne tana fadin, "Babyna, ya kake? Nayi kewarka sosai."
Ta saurara muryar Abbas dake cewa, "Na kasa bacci ne. Na fito daga wanka, naji ba abinda nake son ji face muryarki."
Murmushi Amani tayi tana kallon Aunty Babba, wadda ta kura mata ido. Cikin sanyin murya tace, "Nima haka babyna, yanzu haka maganarka nake ma."
"Are you serious? Zamu yi video call ne. Ina so in ganki cikin sleeping dress din nan naki."
Amani ta kalli Aunty Babba tana jiran amsa, domin wayar tana handsfree. Aunty Babba tayi mata alama da ido cewa ta amsa.
"Eh babyna, a shirye nake. Nima a ƙage nake dana ganka," Amani ta fada.
Aunty Babba tayi murmushi, ta mike ta fita daga dakin tana jin a ranta cewa burinta zai cika.
Dare yayi sosai, Junaid na dakin Abbansu. Ya addabi Abba, ya hana shi sakat. Shi ala dole, ga auta. Suna kwance tare a saman king-size bed dinsa. Junaid ya aza masa kafarsa a saman jikin Abbansu, yana zallar rigima.
"Junaid, dan Allah ka barni na huta. Ka tafi bedroom dinka ka kwanta, ko ka tafi wurin yayyenka ka kwana," Abba ya fada cikin jin bacci.
Cikin shagwaba, Junaid yace, "Nafi jindadin kwanciya a jikinka Abba. In kuma kana so na daina zuwa kwana nan, sai ka dawo da mommynmu."
Rai a bace, Abba yace, "Kada na sake jin ka kira min sunanta"
Cikin zolaya, Junaid yace, "Kai fa kace kana sonta Abba. Ba wanda yayi maka dole. Saboda dadin soyayya, ko su Ammi basu sani ba ka tafi har Amurka ka aurota. Wato kaga kyakkyawa, doguwa, fara mai dogon gashi ko?"
Abban sojoji complete last
Abba ya yunkura tareda fadin "Bismillah," ya janyo pillow, ya shiga bugun Junaid dashi. Dama sun saba, Abba ya maida shi tamkar tsaransa, kuma yana jindadin hakan.
Cikin kukan wasa, Junaid yace, "Abba, dan Allah ka daina, gaskiya na fada. Wallahi Momyn mu akwai kyau, shi ya rudaka."
Cikin_mamaki_Abba_yace, "Wai Junaid, ko saboda_muna_kwana_shimfida_daya_ne_yasa ka_rainani?"
Dariya suka yi gaba dayansu. Duk yadda yaso Junaid ya rufe bakinsa ya daina masa maganar Alexandra, amma ya kiya. Da kyar bacci ya kwashe su duka.