Ba tareda ɓata lokaci ba, gaba ɗayansu suka hallara a wajen zungureren dining table wanda ke ɗauke da kayan maƙwalashe na ci dana sha, mutun goma sha biyu yake ɗauka, sannan akwai kuma wanda Abban su junaid yasa aka ƙara daga cikin wanda aka yi walimar jiya dasu, An ajiye shi a gefen nasu mai mazaunin mutun shida, Aunty azmee ta jera wasu kayan_kalacin a bisanshi, anan Abu sufyan ya zauna tareda su sehrish jahad da kuma hosana,
Tun daga kan yadda kowanne ke kwasar abinci a cikinshi hakan zai tabbatar maka da cewar ba ƙaramar yunwa suke ji ba, ko su Azmee basu jira ta zuba musu ba suka shiga saka abincin da kansu, Sgr ne kawai ta zubawa sae kuma Abbansu, amma sauran duk ba wanda ya tsaya jiranta, nan wurin yayi shiru baka jin hayaniyar komai, sai sautin Cokula dake tashi ƙwas ƙwa-ƙwasss. Abban sojoji book 3.
Ɗagowa Marshal_Omar yayi caraf idonshi suka yi karo dana Hosana, ta zuba mashi idanu ba ko kyaftawa ba tayi, kasancewar teburinsu na kusa dana juna, tazarar dake tsakani kadan ce. Da cokalin dake hannunshi yayi mata nuni da plate din abincin gabanta, alamar ta mayar da hankalinta wajen abinda take ci, murmushi tayi tareda kai hannunta ta dauki lemu tana ɗan korawa.
Junaid kuwa duk ya kasa samun kwanciyar hankali sam ya gaza cin abincin dake gabansa sai faman jujjuya cokalin yake yi a cikin plate, idan ya tuna abinda ya yiwa Jahad a cikin mota a matsayin Sehrish__ sai yaji gabansa na faɗuwa rass, fargabar shi kar jahad ta ɗauka cewa ko ɗan iska ne shi, tunda ba saninshi tayi ba, kar kuma tace zata sanarwa wani abunda ya faru, domin tunawa yayi da yayinda ya bugeta bai sani ba
Abban sojoji book 3 part 2
Hankalinsa a tashe junaid ya miƙe yana ƙoƙarin barin teburin abinci, nan fa hankalin kowa ya koma kansa, har suna haɗa baki wajen tambayarshi ina zai je, fuskarshi cike da damuwa sannan yace "Abba, bana jin yunwa ne, dama munyi break fast tareda Mommy, zanje wurinta ne yanzu" Abbansu yake yiwa magana wanda hankalinshi ke kan Jahad dake shan farfesun da Azmee ta zuba masa a plate, da alama dai ba ƙaramin daɗin wannan farfesun yake yi ba, duba da yadda ta mayar da hankalinta gaba ɗaya kanshi.
OK, zaka iya zuwa," ya bashi amsa, cikin sauri junaid ya kama hanyar da zata kaishi zuwa bedroom ɗin Abbansu domin acan ta sauka, yana tafiya yana waiwaye a ranshi yana cewa "wayyo Allah! ban san me zai biyo baya ba, nasan cewa dole ta sanarwa Uncle abinda nayi mata, idan ta faɗa masa shi kuma nasan zai faɗawa Abban mu ne, Abbanmu zai faɗama Babban yayanmu, shi kuma zai ce eh lallai wuyana ya isa yanka tunda har zan iya bangaje mace daga nan kuma zai yi tunanin turani aikin soja ni kuma abinda bana so, shikenan ni dai tawa ta ƙare.
Jikinta ne ya bata cewa ana kallonta, hakan yasa ta ɗanyi slow daga shan farfesun da take yi, sannan ta ɗan ɗago idanunta, kai tsaye suka haɗa idanu da junaid dake can nesa yana kallonsu, wani sabon mamaki ne ya kamata ganin yadda ya ƙura mata idanu yana kallonta, a ranta tace "ban san meyasa yake kallona ba, tsorona kar ace baya san ganina ne, Allah yasa halinta itaa irin na Sehrish ne, idan ta kasance mai sauƙin kai ce nasan zata rufamun asiri, amma anya za tayi sauƙin kai kuwa?
Nasan me ya kamata inyi daga yau zan dinga ɗaure mata fuska, in nuna tamkar na tsaneta, nasan hakan zai sa taji tsorona taƙi faɗawa kowa abinda ya faru a tsakaninmu! good_idea", yana kai ƙarshen wannan zancen zucin nashi ya galla mata harara tareda murguɗa mata baki, sannan ya juya ya nufi bedroom ɗin abbansu, Jikinta a sanyaye jahad ta ɗauke kanta daga kallon bayansa da take yi, lokaci guda kuma taji komai ya fita daga ranta, ba don komai ba sai irin kallon da taga junaid yayi mata, maganarta ta tabbata, Junaid baya son ganinta, tunda gashi yanzu ya harareta kuma hada murguɗa baki. Abban sojoji book 3.
Muryar abbansu ce ta katseta da cewa "Jahad, meya faru ne? naga kin tsaya da shan farfesun ina fata lafiyarki ƙalau? firgigit ta ɗanyi tareda wurga idonta kanshi tace "Am ok daddy,' jinjina kai yayi kafin yace "Ku saki jikinku, kuci abinci yadda kuke so sosai, kada kuji komai, nasan baku saba ba, don na lura akwai rashin sabo a tare daku, amma nasan a hankali zaku saba da y'anuwanku, Hosana tace "Abba ai ni, dama na saba da kowa, ba kaga yadda na keta cika cikina da abinci ba, jahad ce take jin kunya, ni bana jin kunyar kowa.
Abban sojoji book 3 last
Dariya suka yi gaba ɗaya, Sehrish na cikin yin dariyar nan, Karaf idanunta suka haɗu dana Sgr, ɗagowarshi kenan yayi arba da ita, gabanta ne taji yana faɗuwa rass-rass saboda fuskarshi a murtuke take babu ko alamar annuri, nan take dariyar da take yi ta koma ciki, ganin ta zuba mashi idanu, yasa shi jefa mata harara, cikin sauri ta kawar da idanunta daga kallon fuskarshi, jikinta kuma yayi sanyi, ta shiga tambayar kanta dalilin wannan hararar da taga big bro yayi mata, ko dai baya farinciki ne da kasancewarta JININSA!?tabbas hakan ma zai iya faruwa, Wataƙila ko dan ya saba da ganinta a matsayin ƴar aikinsa, baiwarsa, ƙasƙantacciya shine dalilin da yasa yanzu Yake nuna ɓacin ransa, domin yana ganin tamkar a matsayi ɗaya suke dashi yanzu.
ya'yan Wa da ƙani, da alama hakan bai yi masa ba, "Idan har da gaske ne abinda nake hasashe, in Allah ya yarda zan tattara na bar masu gidansu, saboda bana son abun ɓacin rai, domin masana zai iya yin komai don farin cikinshi, " ta ƙarasa zancen a cikin zuciyarta tareda sake ɗagowa a karo na biyu a hankali don ta saci kallonshi, a yayinda shima ya ƙara ɗagowa da kyawawan idanunsa kai tsaye kuwa suka shiga cikin nata, nan take taji gabanta ya ƙara faɗuwa rass.
Kasa janye idanu yayi daga kallonta da yake, a yayinda yake jujjuya cokalin dake hannunsa a cikin plate ɗin abinci, har zuwa yanzu bai daina mamakin kasantuwarta a matsayin ƴar uwarshi ba, ta jininsa, kamar a cikin mafarki haka yake ganin abun, ganinta zuba mashi ido ba tareda ta janye ba yasa shi ɗaure fuska yasha murrr, saboda kada yarinya taga fuska har tayi tunanin raina masa hankali don ta samu matsayi.
"zaki zauna a matsayin da kike ne, wato wadda take aiki a ƙarƙashina, matsayin da kike dashi kenan, "ya fada a ransa.